Shugaban UNECA ya bukaci ‘yan Afrika da su duba dalilan rikici domin inganta ayyukan tattalin arziki

Babban Sakataren kwamitin tattalin arzikin Afrika na MDD Carlos Lopes, ya bayyana bukatar da ke akwai na ‘yan Afrika su duba ainihin dalilan tashin hankali da rashin tsaro a nahiyar domin samun cigaba da kuma inganta ayyukan tattalin arziki.